Isa ga babban shafi

ECOWAS za ta sake gudanar da taro kan juyin mulkin Nijar

Kungiyar Kasashen Afirka ta wato ECOWAS ta sanya taron shugabanninta a ranar alhamis mai zuwa a birnin Abuja domin nazari akan halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi. 

Zauren taron Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO a birnin Abuja, Najeriya. Ranar 30 ga Yulin 2023.
Zauren taron Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO a birnin Abuja, Najeriya. Ranar 30 ga Yulin 2023. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar yau ta ce shugabannin kasashen da suka fito daga yankin zai duba matakan da ake dauka na diflomasiya da kuma halin da ake ciki ya zuwa wannan lokaci. 

Idan dai ba’a manta ba, shugaban kungiyar Bola Ahmed Tinubu ya aike da tawaga a karkashin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdusalami Abubakar zuwa Nijar, tare da tura wata tawaga a karkashin Ambasada Babagana Kingibe wanda ya ziyarci kasashen Libya da Algeria. 

Bukatar amfani da karfin soja akan sojojin da suka yi juyin mulkin na ci gaba da fuskantar tirjiya daga bangarori da dama, cikin su harda majalisar dattawan Najeriya wadda taki amincewa da bukatar saboda illar sa akan fararen hula. 

Majalisar ta bada shawara ci gaba da daukar matakan diflomasiya domin warware matsalar da kuma mayar da gwamnatin farar hula karagar mulki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.