Isa ga babban shafi

RFI da France 24 sun yi tur da rufe tashoshinsu a Nijar

Gidan rediyon RFI da gidan talabijin na France 24 sun yi Allah-wadai da matakin da hukumomin sojin Nijar suka dauka na dakatar da su daga yada shirye-shiryensu a kasar, mako guda da juyin mulkin da sojojin suka yi a kasar.

Ginin Hukumar Gudanarwar Gidajen Rediyo na RFI da France 24.
Ginin Hukumar Gudanarwar Gidajen Rediyo na RFI da France 24. AFP - KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Hukumar Gudanarwa kafofin yada Faransa a kasashen ketare ta France Medias Monde ta bayyana matakin a matsayin wanda ya yi hannun riga da dokokin shari'a, lamarin da ta ce zai dakile wa 'yan kasar hanyoyin da suke samun cikakkun labarai cikin 'yanci.

Wannan na zuwa ne bayan irin wannan dakatarwar da sojojin da ke mulki a Mali da Burkina Faso suka yi wa RFI da France 24 a watannin da suka shude.

Hukumar ta France Medias Monde ta jaddada kudirinta ga 'yancin yada labarai da kuma kare lafiyar 'yan jaridarta.

RFI na yada shirye-shiryensa a tashoshin FM guda bakwai baya ga gajeren zango  da sauran hanyoyin tauraron dan adam cikin harsunan Faransanci da Hausa da Fulfulde.

Kazalika akwai wasu karin gidajen rediyo 44, abokan huldar RFI da su ma ke yada shirye-shiryensa cikin harsunan Faransanci da Hausa da Fulfulde a Nijar.

A shekarar 2022, wasu alkaluma da aka tattara sun nuna cewa, kimanin masu saurare miliyan 1 da dubu 900 ne ke sauraren RFI a kowanne mako a kasar ta Nijar, wato kwatankwacin kashi 18 na daukacin al'ummar kasar, yayin da RFI din ke zama kafar yada labarai ta ketare mafi girma a kasar kamar yadda wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna.

Har ila yau, alkaluman sun nuna cewa, kimanin rubu'in daukacin jama'ar Nijar ne suka bibiyar tashar ta RFI a kowanne mako a shekarar bara.

Koda yake har yanzu ana iya samun RFI da France 24 ta hanyoyin tauraron dan adam kai tsaye kamar su Eutelsat da Arab-Sat, sai kuma gajeren zango.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.