Isa ga babban shafi

Kotun Kenya ta dakatar da matakin shugaba Ruto na ci gaba da sare itatuwa

Wata kotu a kasar Kenya ta dakatar da matakin shugaban kasar William Ruto na dage haramcin da aka yi kan sare itatuwa, kusan shekaru shida da suka gabata, hukuncin da ke zama babbar nasara ga masu rajin kare gandun daji. 

Wani gandun dajin kasar Kenya.
Wani gandun dajin kasar Kenya. © AFP/Roberto SCHMIDT
Talla

A wannan laraba ce, kotun muhalli da filaye ta kasar Kenyan ta yi umarnin dakatarwar kwanaki 14 kan sokewar da shugaba Ruto ya yi ga dokar hana sare itatuwa da aka bullo da ita tun a shekarar 2018 domin kare gandayen dazukan kasar da kuma dakile bacewar dangogin wasu itatuwa cikin sauri. 

A lokacin da ya dage haramcin a watan Yulin wannan shekara, shugaba Ruto ya ce matakin zai samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, kuma wauta ce a bar manyan bishiyoyi su na rubewa alhali ana shigo da katako daga kasashen waje. 

Kungiyar lauyoyin Kenya ta kalubalanci matakin a gaban kotu, tana mai cewa gwamnati ba da dubi dage haramcin ta fuskar illar haka a kimiyyance ba ko kuma tuntubar al’umma kan tasirinta. 

A hukuncin da ta yanke, mai kwanan wata 1 ga watan Agusta, kotun ta kuma bayar da umarnin dakatar da gwamnati daga bada lasisin sare itatuwan katako. 

Wannan dakatarwar ta kwanaki 14 ne, wato har zuwa loacin ci gaba da sauraron kara kan batun. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.