Isa ga babban shafi

Ruto na Kenya ya shaidawa janar-janar na Sudan su dakatar da shirmen da suke yi

Shugaban Kenya William Ruto ya bukaci janar-janar din Sudan da ke yaki da juna da su dakatar da aika-aikar da suke yi, inda ya yi kira da a sake tunani kan shirin kungiyar Tarayyar Afirka game da magance rikice-rikice a nahiyar.

Shugaban Kenya, William Ruto kenan
Shugaban Kenya, William Ruto kenan AP - Brian Inganga
Talla

Kimanin mutane 1,000 ne aka kashe sannan kusan miliyan daya suka rasa matsugunansu a Sudan tun bayan fadan da aka gwabza tsakanin hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar dakarun kai daukin gaggawa na musamman a cikin watan Afrilu.

"Muna bukatar mu gaya wa wadannan janar-janar su daina shirme," a cewar Ruto yayin wani taron 'yan majalisar dokokin Afirka a Afirka ta Kudu.

Fatan tsagaita bude wuta ya dusashe bayan an keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a makonnin da suka gabata.

Da yake jawabi a wajen taron koli na kasashen Afirka, a birnin Johannesburg, Ruto ya ce lamarin ya nuna gazawar kungiyar AU wajen kawo karshen rikicin.

"Kamar yadda ake yi, ba mu da karfin da za mu iya dakatar da wannan shirme a nahiyarmu," in ji Ruto, ya kara da cewa kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro na AU ya dogara ne kan kudaden waje.

"Muna bukatar mu sake tunani kan kwamitin zaman lafiya da tsaro," in ji Ruto, yayin da yake magana kan hukumar warware rikice-rikice ta AU.

Kasashe mambobin kungiyar sun ba da gudummawar kashi 37 cikin dari na kasafin kudin kungiyar ta AU, bisa ga rahoton kungiyar ta 2021.

Sauran kudaden sun fito ne daga abokan huldar kasa da kasa, ciki har da Tarayyar Turai da wasu kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.