Isa ga babban shafi

Amnesty na zargin kasar Kenya da kuntata wa masu auren jinsi

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta "Amnesty International" tare da wata kungiya da ke kare hakkin masu auren jinsi da ke birnin Nairobi na kasar Kenya, sun ce masu auren jinsi da ke neman mafaka a kasar na fuskantar cin zarafi ciki har da fyade. 

Hoton wasu masu auren jinsi da rufaffen fuskoki.
Hoton wasu masu auren jinsi da rufaffen fuskoki. AP - Ben Curtis
Talla

Rahoton da kungiyoyin suka fitar ya ce ‘yan gudun hijiran da ke sansanin Kakuma a arewa maso yammacin kasar na fuskantar mummunar cin zarafi ba tare da samun dauki daga jami’an ‘yan sanda ba. 

Don haka su ka bukaci gwamnatin Kenya da ta kare hakkin dan adam da kuma dakatar da nuna wariya da masu auren jinsin ke fuskanta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.