Isa ga babban shafi

Tunisia ta hana bulaguro a iyakarta da Algeria bayan tsanantar gobarar daji

Mahukuntan Algeria sun kulle iyakar Oum Teboul da ke tsakanin kasar da Tunisia bayan tashin wata gobarar daji tun a tsakaddaren talatar da ta gabata wadda nta fantsama har cikin dajin Maloula da ke gab da birnin Tarbaka na kan iyakar.

Wutar dajin ta tilasta karkata akalar masu bulaguro a kan hanyar ta iyakar Tunisia da Algeria.
Wutar dajin ta tilasta karkata akalar masu bulaguro a kan hanyar ta iyakar Tunisia da Algeria. REUTERS - STELIOS MISINAS
Talla

Hukumar yaki da bala’o’I ta Tunisia ta ce jami’an kashe gobara na kasar na ci gaba da kai dauki don dakile fantsamarta amma har zuwa daren jiya laraba ba a iya kaiwa ga nasarar shawo kan wutar dajin ba.

Tuni dai mahukuntan Tunisia suka hana duk wata zirga-zirga da za ta ratsa da mutane ta kan iyakar ta Oum Teboul yayinda aka karkatar da bulaguron matafiyan da ke kan hanya zuwa iyakar Babbouch da El Aioun.

Gobarar dajin dai na da nasaba da tsananin zafin da kasashen arewacin Afrika ke fuskanta a cikin watan nan na Yuli.

Sanarwar da gwamnatin Tunisia ta fitar ta roki ilahirin matafiyan da ke shirin bulaguro su kaucewa shiga hanyar mai hadari, yayinda a bangare guda ma’aikatar lafiyar kasar ta roki masu lalura da mata masu juna biyu da kuma kananan yara su kaucewa fita rana don tsira da lafiyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.