Isa ga babban shafi

An kashe gobarar dajin da ta lakume rayuka a Algeria

Hukumomin Algeria sun yi nasarar kashe gobarar dajin da ta lakume rayukan mutane akalla 38 da suka hada da kananan yara 10 a yankin arewacin kasar kamar yadda jami’an kwana-kwana suka sanar a wannan Juma’ar.

Gobarar dajin ta yi barna tare da lakume rayuka akalla 38 a Algeria
Gobarar dajin ta yi barna tare da lakume rayuka akalla 38 a Algeria REUTERS - RAMZI BOUDINA
Talla

'Yan Algeria da ke zaune a cikin kasar da wadanda ke rayuwa a kasashen ketare, sun yi ta har-hada riguna da magunguna da abinci domin taimaka wa mutanen da lamarin ya shafa.

Kazalika akwai  masu aikin ceto na musamman da ke agaza wa mutanen da suka  rasa gidajensu da dukiyoyinsu sakamakon ibtila’in gobarar.

Babban Jami’in hukumar kashe gobarar, Kanar Farouk Achour ya ce, sun yi nasarar kashe wutar baki dayanta.

Ibtila'in gobarar daji ya zamo tamkar al’ada da ke faruwa a duk shekara sakamakon matsalar sauyin yanayi da ta yi kamarai tare da haddasa fari a kasar.

Tun daga farkon watan Agustan wannan shekarar, akalla an samu tashin gobarar daji har sau 150 a kasar, inda ibtila’in ya cinye daruruwan kadada.

Kimanin jami'an kwana-kwana dubu 1 da 700 aka jibge tsakanin ranakun Laraba zuwa Alhamis domin aikin kashe gobarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.