Mutane 49 sun mutu a Kenya sanadiyar hadarin mota
Akalla mutane 49 ne suka mutu, a wani mummunar hadarin babbar motar dakon kaya da ke dauke da sundukai, a mahadar Londiani kusa da birnin Kericho, kamar yadda ministan sifirin kasar Kipchumba Murkomen, ya shaidawa manema labarai a yau Asabar.
Wallafawa ranar:
Babban jami’in ‘yan sandan yankin Geoffrey Mayek ya ce, kimanin wasu mutum 30 sun samu raunika, haka nan akwai wasu mutum biyu da ke makale ba’a ceto su ba.
Shugaban kasar William Ruto ya mika sakon ta’aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
Kenya na daya daga cikin kasashen Afrika da ke fama da matsalar hadarin mota, domin a cewar alkaluman da hukumar kare aukuwar hadura ta kasar ta fitar, sun nuna cewar a shekarar da ta gabata kadai mutane dubu 21 da dari 760 ne hadarin mota ya rutsa da su, daga cikin wancan adadi mutane dubu 4 da dari 690 suka mutu.
A wani rahoton da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar a watan Satumbar shekarar da ta gabata, ya ce nahiyar Afrika ce ke kan gaba wajen aukuwar hadara a duniya, inda mutane sama da dari 8 ke mutuwa a kowace rana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu