Isa ga babban shafi

Kenya ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da EU don saukaka fitar da amfanin gonarta

Kenya da Tarayyar Turai sun cimma yarjejeniyar kasuwanci da zai ba ta damar fitar da kayayyakin amfanin gonarta ba tare da biyan haraji ba. Yarjejniyar da ke zuwa a daidai lokacin da Turai ke neman karfafa dangantaka ta tattalin arziki da nahiyar Afrika, da zummar yi wa China zarra.

Tawagar Tarayyar Turai da mahukuntan Kenya yayin wata yarjejeniyar kasuwanci da aka cimma a Nairobi. 19/06/19
Tawagar Tarayyar Turai da mahukuntan Kenya yayin wata yarjejeniyar kasuwanci da aka cimma a Nairobi. 19/06/19 © Hussein Mohamed
Talla

 

Shugaban Kenya, William Ruto ne ya jagoranci wani biki na musamman a birnin Nairobi don marhabun da wannan yarjejeniya ta tattalin arziki da kasarsa ta kullla da Tarayyar Turai. 

Watanni bakwai aka yi kafin cimma wannan yarjejeniya, lamarin da ya maishe  ta  yarjejeniya  mafi sauri da Tarayyar Turai ta taba cimma, kamar yadda  jami’ai daga dukkan bangarorin suka bayyana. 

A karkashin yarjejeniyar, za a kuma  sassauta haraji a kan kayayyakin Turai da ke shigowa Kenya na tsawon shekaru 25, kamar yadda  jami’an suka bayyana, a yayin sanya hannu a yarjejeniyar a birnin Nairobin Kenya. 

Kenya, kasa ta bakwai a karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, ita ce wadda ta fi samar da ganyen shayi, kofi, furanni da ganyayyaki, kuma Turai ce ke sayen kaso 21 na dukkannin kayayyakin da take fitarwa. 

A shekarar 2016, Kenya ta taba sanya hannu a yarjejeniya makamancin wannan da kawayenta na gabashin Afrika, sai dai ba ta kan-kama ba saboda ba dukkanin kasashen ne suka sanya hannu a cikinta ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.