Isa ga babban shafi

Kenya ta lafta wa jama'ar kasar haraji don farfado da tattalin arziki

Shugaban Kenya William Ruto ya amince da fara aikin sabuwar dokar kara yawan harajin da gwamnati ke caza akan wasu muhimman lamurran da suka shafi al’ummar kasar ciki har da man fetur da kuma kudaden hayar gidaje. 

Shugaban Kenya, William Ruto.
Shugaban Kenya, William Ruto. © REUTERS/Michele Tantussi
Talla

Sabuwar dokar harajin da majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar amincewa da ita a makon jiya, ta ninka yawan harajin da ke kan farashin man fetur zuwa kashi 16 cikin 100 da kuma kara yawan kudaden gidajen haya, matakin da masu caccakar gwamnati suka ce babu abin da zai haifar illa jefa al’ummar Kenya marasa karfi cikin karin kunci bayan wanda suke ciki na fuskantar tsadar farashin kayayyaki. 

Shugaba William Ruto da ya hau kan karagar mulki a watan Satumba, ya dukufa wajen laluben hanyoyin sama wa gwamnati kudaden shiga domin farfado da tattalin arzikinta da ya durkushe, matsalar da ya gada daga magabacinsa Uhuru Kenyatta. 

Yayin kare sabuwar dokar kara harajin, Ruto ya ce hakan zai bai wa gwamnati damar samun karin kudaden shigar da  yawansu zai zarce dala biliyan 2 a duk shekara. 

A yanzu haka dai yawan bashin da ke kan kasar Kenya ya kai kusan dala biliyan 70, yayin da adadin kudin ruwan da take biya ya hauhawa bayan da darajar kudin kasar na Shilling ta fadi zuwa guda 140 kan kowace dalar Amurka guda. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.