Isa ga babban shafi

'Yan kasar Mali na kada kuri'u a zaben raba gardama kan kundin tsarin mulki

A wannan Lahadin, al’ummar Mali ke kada kuri’u don amincewa ko akasi ga sabon kundin tsarin mulkin kasar, a matsayin wani muhimmin mataki na farko wanda zai ga shirin komawa ga mulkin farar hula a watan Fabrairu mai zuwa.

Masu jefa ƙuri'a a zaben raba gardamar za su zaɓi tsakanin farar kati wanda ke nuna cewa ana goyon bayan sabon Kundin Tsarin Mulki, ko kuma jan kati da ke nuna adawa da shirin.
Masu jefa ƙuri'a a zaben raba gardamar za su zaɓi tsakanin farar kati wanda ke nuna cewa ana goyon bayan sabon Kundin Tsarin Mulki, ko kuma jan kati da ke nuna adawa da shirin. © Sia KAMBOU-AFP/ Montage RFI
Talla

Kundin tsarin mulkin Mali dai tun a shekarar 1992, ake amfani da shi, kuma ya fuskanci tirjiya so da dama a duk wani yunkuri da na gyara shi.

Masu kada kuri'u

Sama da masu kada kuri’a miliyan 8.4 ne ake saran su fito runfunan zabe tun daga karfe 8 na safe domin wannan zaben raba gardama.

Masu jefa ƙuri'a za su zaɓi tsakanin farar kati wanda ke nuna cewa ana goyon bayan sabon Kundin Tsarin Mulki, ko kuma jan kati da ke nuna adawa da shirin.

Juyin mulki

A wannan zabe na farko da sojoji suka shirya tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Kéïta da aka fi sani da IBK a watan Agustan 2020, akwai kalubale da dama da za a fuskanta.

Babu zabe a wasu sassa

Daga cikin kalubalen, akwai shirya zaben raba gardama a duk fadin kasar. Wasu gungun masu dauke da makamai da ke da hannu a shirin samar da zaman lafiya sun yi watsi da daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar tare da sanar da cewa ba za a kada kuri'a a yankunan arewacin da suke iko da su ba. Don haka, hankula zasu karkata zuwa yankin Kidal.

Kungiyoyin masu ikirarin jihadi sun yi barazanar hana gudanar da ayyukan zabe a wasu wuraren.

 A nata bangaren gwamnatin kasar Mali ta tabbatar da cewa, an yi dukkan shirye-shirye domin gudanar da zaben cikin lumana. Tun bayan zuwan sojoji kan karagar mulki a shekarar 2020, wannan shi ne karon farko da Kanar kuma shugaban rikon kwarya Assimi Goïta ke fuskantar ‘yan kasar a runfunar zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.