Isa ga babban shafi

An kammala gangami kan zaben raba gardamar kundin tsarin mulkin Mali

Yau juma'a ake karkare gangamin wayar da kai game da zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin Mali wanda al'ummar kasar ke shirin kadawa kuri'a a lahadin da ke tafe.  

Wasu 'yan kasar Mali.
Wasu 'yan kasar Mali. © MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Zaben shi ne na farko da sojoji suka shirya tun bayan da suka kwace mulki a watan Agustan shekarar 2020, biyo bayan matsalolin tsaro, rikicin siyasa da koma bayan tattalin arzikin da kasar ta Mali ta tsinci kanta a ciki, kalubalen da har yanzu ba a kammala magancewa ba. 

A watan Maris na shekarar 2024 sojojin da ke mulkin Mali suka yi alkawarin sake mika wa farar hula mulki, bayan kammala zaben da za su shirya a watan fabarairu. 

Sai dai kasa da watanni tara kafin cikar wa'adin, har yanzu karin haske kan rawar da sojojin za su taka a nan gaba, shugaban mulkin sojan, Kanal Assimi Goita, wanda wasu ke rade-raden zai sanya rigar farar hula don neman yin tazarce. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.