Isa ga babban shafi

An fara shirin gudanar da zaben raba gardama kan kundin tsarin mulkin Mali

Al’ummar Mali sun fara shirin tunkarar zaben raba gardama kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar da aka kwashe tsawon lokaci ana dako.

Wasu 'yan kasar Mali.
Wasu 'yan kasar Mali. © MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Sojojin da ke mulki sun ce sabon kundin tsarin mulkin ya kunshi shawarwari da dama wadanda talakawa suka bayar, sai dai wasu na cike da fargaba kan yiwuwar sabon kundin ya bai wa shugaban kasa karfin fada aji fiye da kima.

A ranar 18 ga watan da muke ciki ne ake shirin gudanar da zaben raba gardamar, wanda aka kaddamar da gangamin wayar da kai a kansa tun a ranar Juma’ar da ta gabata.

An dai shafe shekaru ana kokarin gyara kundin tsarin mulkin Mali, abinda ya sa aka taba tsayar da  watan Yuli a matsayin lokacin da za a gudanar da zaben raba gardama kan sauyin, amma aka rika dage shirin a lokuta da dama.

A shekarun baya dai an sa ran cewa sabon kundin tsarin mulkin da aka yi yunkurin samar wa, zai bayar da damar kirkirar yankuna, kamar yadda hakan ke kunshe a cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin gwamnati da mayakan ‘yan tawayen Azbinawa a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.