Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Mali ta kafa hukuma da zata tsara sabon kundin tsarin mulki

Gwamnatin sojin Mali, ta sanar da kafa wata hukumar da za ta tsara sabon kundin tsarin mulki, bayan tsawaita wa'adin mulkin soja har zuwa shekara ta 2024.

shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita.
shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita. © AFP
Talla

Sanarwar da shugaban kasar Asimi Goita ya fitar da yammacin Jumma’a, ta nuna cewa hukumar za ta samu watanni biyu kafin ta kammala aikin ta.

Sanarwar ta ce hukumar za ta kunshi shugaban kasa, da wakilai biyu da masana kuma za ta tuntubi jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula, da masu dauke da makamai wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati, da shugabannin addinai da na gargajiya da kuma kungiyoyin kwadago.

Wa'adin mika mulki

A ranar Litinin ne shugaban mulkin sojan kasar Kanar Assimi Goita ya rattaba hannu kan wata doka da ta ce sojoji za su tafiyar da mulkin kasar har zuwa watan Maris din shekarar 2024, lokacin da za a gudanar da zabe.

Matakin ya dakile yunkurin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ke yi na gaggauta mika mulki ga fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.