Isa ga babban shafi

Za'a yi zanga-zangar adawa da zaben raba gardama a Mali

Gwamnatin mulkin sojin kasar Mali na fuskantar sabuwar zanga-zangar domin nuna adawa da shirin zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki dake tafe ranar 18 ga watan Yuni.

Shugaban rikon kwaryar sojin Mali kanal Assimi Goïta 22/09/22
Shugaban rikon kwaryar sojin Mali kanal Assimi Goïta 22/09/22 AFP - OUSMANE MAKAVELI
Talla

Masu adawa da matakin da suka kira gagarumin zanga-zanga sun bukaci gagauta gudanar da zabe da kuma mika mulki ga farar hula.

Gyaran kundin tsarin mulkin kasar Mali shi ne babban mataki na farko da sojoji suka dauka tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan 2020 a shirye-shiryen su na tabbatar da ci gaba da rike madafun mulki har zuwa shekarar 2024.

Cikin wata sanarwa kungiyar ta ce kuri'ar raba gardamar ta sojoji ke shirin gudanawa ya saba ka’ida kuma wuce gona ne da iri, abin da ya kamata kawai a shirya babban zabe, domin maida mulki ga farar hula.

Kiran na ranar 20 ga watan Fabrairu wani yunkuri ne na kungiyoyi da wasu jiga-jigai da suka nisanta kansu da gwamnatin soji na hada kan jam’iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.