Isa ga babban shafi

Rikicin Sudan ya bazu zuwa garuruwan yammacin kasar

Fada ya barke garuruwa da dama da ke yammacin Sudan a ranar Laraba, lamarin da ya tabbatar da fadadar gumurzun da ke gaba da kazanta tsakanin sojojin gwamnati masu biyayya ga shugaba Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa Muhd Hamdan Daglo.

Wani yanki a kudancin Khartoum, babban birnin kasar Sudan.
Wani yanki a kudancin Khartoum, babban birnin kasar Sudan. AFP - -
Talla

Yayin da yake karin bayani akan halin da ake ciki, gwamnan jihar Darfur ta Yamma Khamis Abbakar, ya yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta kai musu dauki domin dakatar da abinda ya kira da kisan kare dangin da ake yi a kasar ta Sudan.

A cewar gwamnan adadin fararen hular da a yanzu ke rasa rayukansu ya wuce kima, biyo bayan hare-haren da hadin gwiwar dakarun RSF da suka bijirewa gwamnati da mayakan sa-kai suka kaddamar a yankunan El Geneina, inda ‘yan kabilar Masalit ke zaune, fadan da ya bazu zuwa daukacin yankunan birnin.

Wata kididdigar kungiyoyin fararen hula ta bayyana cewar, akalla mutane 1,100 aka kashe a Sudan, tun bayan barkewar rikicin kasar a tsakiyar watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.