Isa ga babban shafi

Masu rikici da juna sun amince da tsagaita bude wuta a Sudan

Bangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun amince da tsagaita bude wuta a fadin kasar na tsawon sa'o'i 24, kamar yadda masu shiga tsakanin Saudiyya da Amurka suka sanar, matakin da ya fara aiki karfe shida na Safiya agogon kasar.

Janar Abdel-Fattah Burhan kenan lokacin da ya ziyarci dakarun gwamnati a Khartoum, ranar 30 ga watan Mayu, 2023.
Janar Abdel-Fattah Burhan kenan lokacin da ya ziyarci dakarun gwamnati a Khartoum, ranar 30 ga watan Mayu, 2023. © AP
Talla

Yarjejeniyar dai ta kasance na baya bayan nan a yunkurin da aka yi na dakatar da fadan da aka kwashe makonni ana gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da mayakan sa kai na RSF.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, bangarorin biyu sun amince kamar yadda suka yi a yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka yi a baya, na kauracewa fadada ayyukan soji a tsawon sa'o'i 24, da kuma hana zirga-zirga, kai hare-hare, amfani da jiragen sama ko jirage marasa matuka, tashin bama-bamai da kuma hare-haren bindigogi.

Har ila yau, Janar-Janar din sun amince da ba da damar zirga-zirgar ba tare da tsangwama ba tare da isar da kayan agaji a duk fadin kasar.

Masu shiga tsakani sun ce sun ba da shawarar tsagaita wuta na baya-bayan nan a wani yunkuri na karya lagon tashe-tashen hankula da suka haifar da bala'in jin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.