Isa ga babban shafi

Sudan: An kwashe yaran da suka rage a gidan marayun Khartoum bayan mutuwar 70

An kwashe sauran yaran da suka rage a wani gidan marayu dake babban birnin kasar Sudan sakamakon mutuwar jarirai sama da 70 da yara kanana da manya saboda yunwa da rashin lafiya cikin watanni biyu da suka gabata.

Wasu jarirai da ke gidan marayun da aka sauyawa matsuguni a Sudan.
Wasu jarirai da ke gidan marayun da aka sauyawa matsuguni a Sudan. © AFP
Talla

Lamarin da ya faru a gidan marayu na Al-Mayqoma labarin halin da yaran ke ciki ya yi ta yamadidi a watan da ya gabata yayin da ake gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai na Rapid Support Forces.

Mutuwar dai ta bayyana irin barnar da aka yi wa fararen hula tun tsakiyar watan Afrilu lokacin da fadan ya barke tsakanin dakarun da ke biyayya ga Janar Abdel-Fattah Burhan da dakarun RSF karkashin jagorancin Janar Mohammed Hamdan Dagalo.

Kimanin yara 300 a gidan marayu na Al-Mayqoma da ke birnin Khartoum aka sauyawa wuri a wani wuri da ke arewa maso gabashin Afirka, in ji Ricardo Pires, kakakin hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF.

“Ma'aikatun kula da walwalar jama’a da na kiwon lafiya na Sudan sun dauki nauyin kula da yaran, yayin da UNICEF ke bayar da tallafin jin kai da suka hada da kula da lafiya, abinci, ayyukan ilimi da kuma nishadantarwa,” in ji Pires.

Ya ce yaran na karbar kulawar likitoci bayan doguwar tafiya da suka yi zuwa sabon wurin da suke.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa, wacce ta taimaka wajen kwashe mutanen, ta ce an samar da masu kula da yaran guda 70 a sabon wurin da aka kebe musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.