Isa ga babban shafi

Masar ta tsaurara wa 'yan Sudan hanyoyin shiga kasar

Masar ta sanar da tsaurara ka'idojin shiga kasarta ga 'yan kasar Sudan, kasar da ta shafe kusan watanni biyu cikin kazamin fada da ake gwabzawa ya haifar da mummunar matsalar jin kai.

Shugaban kasar Masar Abdel Fatah El sisi
Shugaban kasar Masar Abdel Fatah El sisi © Mandel Ngan / AP
Talla

Tun farkon rikicin kasar Sudan, a ranar 15 ga watan Afrilu, tsakanin sojojin gwamnati da dakarun sa-kai na RSF kimanin 'yan kasar dubu 200 da suka tsere daga yakin sun shiga Masar, akasari ta hanyar mota.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da sabbin matakai na tsarin shigar makwabtansu cikin Masar.

Ya zuwa yanzu hukumomin Masar sun kebe mata da yara ‘yan kasa da shekaru 16 da sauran ‘yan Sudan masu sama da shekaku 50 daga wadanda ke bukatan biza kafin shiga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.