Isa ga babban shafi
Sudan-Masar

HRW ta zargi 'yan sandan Masar da cin zarafin ‘yan gudun hijirar Sudan

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta zargi ‘yan sandan Masar da cin zarafin ‘yan gudun hijirar Sudan da suka samu mafaka a cikin kasar.

Yadda jami'an tsaro ke wahalar da 'yan cirani.
Yadda jami'an tsaro ke wahalar da 'yan cirani. REUTERS/Eric Gaillard
Talla

A rahoton da ta fitar, kungiyar ta HRW ta ce ‘yan sandan na Masar sun kama ‘yan gudun hijira da kuma masu neman mafaka akalla 30 tsakanin watan disambar 2021 zuwa farkon wannan shekara, inda tsare tare da azaftar da su.

Rahoton kungiyar ya dogara da shaidar da ta samu daga ‘yan gudun hijira uku da kuma wata kungiyar kare hakkin dan adam da ke birnin Alkahira ne, wadanda suka tabbatar da cewa an cafke mafi yawan mutanen ne a cikin gidajensu yayin da aka cafke sauran a wuraren shan shayi.

Bayan kama su, ‘yan sandan sun yi wa mutanen duka tare da sanya su aikin karfi, ciki har da tilasta masu lodawa da kuma sauke kaya a kan manyan motoci ba tare da an biya su ko sisin kobo ba, kuma suna wannan aiki tsakanin karfe 8 na dare zuwa 3 na asuba.

Mataimakin shugaban ofishin kungiyar ta Human Rights Watch a yankin Gabas ta Tsakiya Joe Stork, ya bukaci mahukuntan kasar ta Masar da su binciki wadanne zarge-zarge tare da hukunta wadanda aka sama da laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.