Isa ga babban shafi

Minti 10 bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan, rikici ya sake barkewa

An ci gaba da gwabza rikici a babban birnin Sudan Khartoum a ranar Lahadin nan, bayan karewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon awa 24 da bangarorin da ke rikici da juna suka cimma.

Hayaki da ke tashi a wasu sassan Khartoum babban birnin kasar Sudan yayin fafatawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar RSF da suka bijire.
Hayaki da ke tashi a wasu sassan Khartoum babban birnin kasar Sudan yayin fafatawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar RSF da suka bijire. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Yarjejeniyar ta taimaka wajen baiwa mazauna birnin Khartoum damar fita don sayen kayan abinci da kuma isar da kayan agaji wasu bangarori.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewar minti 10 bayan karewar wa’adin yarjejeniyar a ranar Lahadin nan, aka fara jin karar fashe-fashe a birnin da ya kwashe tsawon Asabar ba tare jin su ba.

A baya ansha cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin masu rikici da juna, ciki kuwa harda wacce Amurka ta yi barazanar sanyawa Janar Janar din takunkumi amma sai dai haka bata cimma ruwa ba.

Tun bayan faro rikicin a tsakiyar watan Afrelun da ya gabata, mutane kusan dubu daya da dari 8 ne suka rasa rayukan su, ya yin da kusan mutane miliyan biyu suka bar muhallin su ciki kuwa harda mutane dubu dari 476 da ke gudun hijira a kasashe da ke makwafta da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.