Isa ga babban shafi

Birnin Khartoum ya yi tsit bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta

Sa’oi kadan bayan kaddamar da yarjejeniyar tsagaida wuta ta tsawonan awo 24 a Sudan, birnin Khartoum da ake gwabza rikici a cikin sa tsakanin sojojin kasar da kuma na kai dauki na RSF ya yi tsit a asabar din nan.

Yadda mazauna birnin Khartoum suka fito don yin sayayya a kasuwanni, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta awa 24,
Yadda mazauna birnin Khartoum suka fito don yin sayayya a kasuwanni, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta awa 24, © AFP
Talla

Yarjejeniyar da ta fara aiki da misalin karfe 6 na safe agogon kasar karfe 4 ke nan agogon GMT, na cikin matakan da kasashen Amurka da Saudiya ke dauka na ganin an tsagaita rikicin don samun damar shigar da kayan agaji cikin kasar.

Haka nan, ana ganin yarjejeniyar za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin da aka faro a ranar 15 ga watan Afrelun da ya gabata, tsakanin shugaban rundunar sojojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma kwamandan rundunar kai dauki da RSF Modamed Hamdan Dagalo.

A baya dukkanin yarjejeniyar tsakaita wutar da aka kulla bata yi tasiri ba, inda bangarorin ke zargin juna da karya ta.

Wani mazaunin Arewacin birnin Khartoum Mahmud Bashir, ya ce suna sanya ido don ganin yadda matakin zai dore, wanda zai basu damar fitowa don nemo kayan abinci da kuma na masarufin da suke bukata.

Mazauna birnin dai na fatan wannan yarjejeniyar ta awo 24, ta bada damar shigar da kayan agaji musamman na magunguna ga wadanda suke cikin tsananin bukata da kuma wadanda suka samu raunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.