Majalisar dokokin Libya ta zargi gwamnati da yunkurin kashe dan majalisa
Majalisar dokokin Libiya da ke gabacin kasar ta zargi gwamnatin kasar mai hedkwata a Tripoli da kai hari gidan daya daga cikin ‘yan majalisarta ta hanyar amfani da jirgin yaki mara matuki.
Wallafawa ranar:
Sai dai da take sanar da matakin, gwamnatin hadin kan kasa da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a Libya, ta ce hare-haren sun shafi maboyar wasu gungun masu fasa kwaurin man fetir da kwayoyi da kuma mutane ne a kewayen Zawiya da ke gabar tekun Bahar Rum a yammacin babban birnin kasar.
Ta ce harin bisa umurnin Firanministan rikon kwarya Abdulhamid Dbeibah ya yi nasara a kan wadandan bata gari.
Sai dai majalisar da ke da mazauni a gabashin kasar, ta ce harin da aka kai an kai shi ne gidan dan majalisar Zawiya Ali Bouzribah, mai adawa da gwamnatin Dbeibah.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu