Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta kama hanyar warware rikicin shugabancin Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, Kwamitin Hadin-guiwa tsakanin Majalisar Wakilan Libya da Majalisar Shata Kundin Tsarin Mulkin Kasar, sun cimma matsaya ta farko kan wasu ayoyin dokar kasar har guda 137.

Mataimakiyar Musamman ga Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Siyasa a Libya Stephanie Williams yayin halartar taron tattaunawa kan siyasar kasar a birnin Tunis, na kasar Tunisia Nuwamba 9, 2020.
Mataimakiyar Musamman ga Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Siyasa a Libya Stephanie Williams yayin halartar taron tattaunawa kan siyasar kasar a birnin Tunis, na kasar Tunisia Nuwamba 9, 2020. REUTERS - ZOUBEIR SOUISSI
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar, mai bai wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya shawara, Stephanie Williams ta bayyana farin cikinta kan yadda bangarorin biyu suka amince da babi na biyu da ke magana kan ‘yanci  da kuma wani bangare da ke magana kan karfin shari’a.

Tuni dai Firaministan Libya da Majalisar Dokokin Kasar ta zaba, wato Fathi Bashaga ya ce, wannan tagomashin zai  bada damar mika mulki ta hanyar gudanar da zaben da al’ummar kasar suka yi na’am da shi.

A cikin watan Maris ne, Mai bai wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar shawarar, ta gayyaci Majalisar Wakilan da Majalisar Shata Kundin Tsarin Mulkin Kasar domin ganin sun zabi mambobi shida-shida a tsakaninsu da za su kasance wakilai a cikin kwamitin na hadin guiwar da aka dora wa alhakin tsara kundin tsarin mulkin kasar ta Libya.

Rudanin siyasa

Siyasar Libya dai ta shiga rudani a cikin watan Disamba sakamakon wargajewar shirin gudanar da zabe, inda bangarorin da ke adawa da juna suka yi ta yi wa juna zagon-kasa.

A bangare guda, a Talatar da ta gabata, an ji karar harbe-harben bindiga a babban birnin Tripoili a daidai lokacin da Firaminsta Bashaga ya yi yunkurin kifar da gwamnatin abokin adawarsa kuma Firaminista mai rikon kwarya Abdulhamid Dbeibah, lamarin da ke dada barazanar kazancewar rashin zaman lafiya a kasar wadda tuni yaki ya daidaita ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.