Isa ga babban shafi

Gwamnatin yan adawar Libya ta gudanar da zaman ta na farko

Gwamnatin ‘yan adawar Libya da majalisar  gabashin kasar ta kafa, ta gudanar da zamanta na farko don kalubalantar gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan majalisar dinkin duniya da ke Tripoli.

Taron sassanta yan siyasar kasar Libya  a Masar
Taron sassanta yan siyasar kasar Libya a Masar Présidence égyptienne / AFP
Talla

Kasar ta Libya da ke fama da rikici, na da gwamnatoci biyu ne a cikin ta tun a watan Fabuwairu, inda majalisar kasar ta ambata tsohon ministan harkokin cikin gida Fathi Bashagha a matsayin sabon fara ministan kasar.Nadin nasa dai na zuwa ne a matsayin adawa da na Abdulhamid Dbeibah wanda majalisar dinkin duniya ke goya baya.

Taswirar kasar Libya
Taswirar kasar Libya © RiskIntelligence

A lokacin taron da tsagin Bashagha suka gudanar a ranar Alhamis din nan, sunce suna aikine don sauke nauyin da ya rataya a wuyan su a matsayin su na ‘yan majalisa.

Tsagin gwamnatin da aka samu dai shine na baya-bayannan a kasar a siyasan ce tun bayan faduwar gwamnatin tsohon shugaban kasar Mummer Gaddafi a shekarar 2011.

Firaminista mai rikon kwariya   Abdelhamid Dbeibah a Tripoli
Firaminista mai rikon kwariya Abdelhamid Dbeibah a Tripoli © Mahmud TURKIA / AFP

A dai ranar laraba ce akaji Bashagha na cewa a shirye yake ya yafa aiki a ofishinsa, lamarin da ya fuskanci turjiya daga Abdulhamid ya na mai cewar zai mika gwamnati ne kadai ga zababbiyar gwamnati.

Shi dai Bashagha na samun goyon bayan Khalifa Haftar ne, babban kwamandan da ya jagoranci kwace ikon Tripoli a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020.

Samar da gwamnati biyu a kasar Libya da aka yi a tsakanin shekarar 2014 da kuma 2021 ya kara rura wutar rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.