An yi artabu tsakanin magoya bayan jagororin Libya
Rikici ya barke a babban birnin Tripoli na Libya tsakanin magoya bayan bangarorin da ke muliki a kasar a wannan Talatar, inda suka shafe tswon sa’o’i suna artabu.
Wallafawa ranar:
Kawo yanzu babu bayanai game da irin barnar da wannan arangama ta haddasa tsakanin bangarorin biyu da basa-ga-maciji a kasar ta Libya mai arzikin man fetur.
Libya dai ta jima karkashin mulkin Firaminista Abdulhamid Dbeibah, amma ya fuskanci kalubale daga Fathi Bashaga, da Majalisar Dokoki ta ayyana a matsayin wani Firaministan na daban a cikin watan Fabairu a yankin gabashin kasar, inda kuma ya samu goyon bayan Khalifa Haftar.
Rikicin dai ya barke ne tun ma gabanin bullowar alfijir bayan da jami’an yada labarai na Firaminista Bashaga suka sanar da isowarsa birnin Tripoli cikin rakiyar wasu ministocinsa domin fara aiwatar da wani aiki.
Ana fargabar cewa, wannan sabon tashin hankalin zai sake haddasa makamancin rikicin da aka gani a 2011 bayan Kungiyar Tsaro ta NATO ta goyi bayan juyin juya halin da ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin Moammar Gaddafi da kuma fadan da ya barke a 2019-2020, lokacin da magoya bayan Haftar suka kai hari a babban birnin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu