Isa ga babban shafi

Kananan 'yan sandan Ghana sun maka gwamnati a kotu

Jami’an ‘yan sandan Ghana 82 sun shigar da karar gwamnatin kasar sabida gazawar ta wajen kara musu girma bayan kammala karatun da ya kamata. 

Wasu jami'an 'yan sandan kasar Ghana a birnin Accra.
Wasu jami'an 'yan sandan kasar Ghana a birnin Accra. © AP - Sunday Alamba
Talla

‘Yan sandan karkashin jagorancin mataimakin sifeta Kofi  Osal, sun ce anki kara musu girma sannan kuma an hanasu shiga kwalejin horas da ‘yan sanda bayan kammala karatu tun a zangon shekarar 2017/2018. 

Sun ce sun shigar da karar ne inda suke bukatar kotun da ke Accra ta umarci hukumar kula da aikin ‘yan sandan kasar ta kara musu girma. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.