Isa ga babban shafi

Akufo-Addo ya kai ziyarar farko Burkina Faso tun bayan rikicin su kan Wagner

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya kai ziyarar farko ga makobciyar kasar sa ta Burkina Faso tun bayan da aka samu  wata tangarda tsakanin kasashen biyu sakamakon wasu kalamai da shugaban na Ghana yayi akan alakar sojojin hayar Rasha na Wagner da kasar ta Burkina. 

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. 23/09/21
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. 23/09/21 AP - Jacquelyn Martin
Talla

Shugabannin kasashen biyu sun gudanar da taro ne a kebe ba tare da barin ‘yanjarida halartar sa ba, amma fadar shuagaban ta baiyana cewa Akufo-Addo ya gana da shugaban mulkin sojin kasar kaftin Ibrahim Traore dangane da wasu muhimman batutuwa da suka jibanci matsalolin tsaro. 

Shugaban na Ghana na wannan ziyarar ce bayan watanni 6 da Alakar kasashen biyu tayi tsami sakamakon wata ganawar sa da sakataren harkokin wajen Amurka Antoni Blinken, inda yake cewa Burkina Faso ta kammala shirin aiki da sojojin hayar Wagner kamar yadda Mali ta yi, a kokarin ta na kawar da ta’addanci a kasar. 

Akufo-Addo ya ce Burkina zata biya su ne da ma’adanai da kasar ke da arzikin su, inda ya kara da  cewar sojin na Wagner na kan iyakar kasashen su. 

A wannan lokaci nan take Barkina Faso ta yi Allah wadai da kalaman nasa tare da janye jakadan ta dake Ghana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.