Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta musanta zargin jibge kayayyakin yakin Wagner a kasar

Shugaban gwamnatin Sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya musanta rade radin da ke cewa gwamnatinsa ta katse huldar Diflomasiyya tsakaninta da Faransa wanda ya bukaci ta janye Sojinta daga kasar ba tare da bata lokaci ba. 

Shugaban gwamnatin Sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahima Traoré.
Shugaban gwamnatin Sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahima Traoré. © Kilaye Bationo / AP
Talla

A wani jawabinsa Kyaftin Traore ya musanta cewa Sojojin hayar kungiyar Wagner na Rasha sun girke dakaru da kayakin yaki a cikin kasar.

Faransa da ke matsayin uwar goyon Burkina Faso, ta na da tarin dakaru da ta girke a sansani na musamman wadanda ke taimakawa kasar ta yankin Sahel yaki da ta'addanci sai dai a baya-bayan nan ana ganin takun saka tsakanin kasashen biyu da ya kai ga bukatar janye dakarun.

Gidan talabijin na Burkinabe mallakin gwamnatin kasar ya haska shugaban gwamnatin sojin Kaftin Ibrahim Traore na cewa tabbas akwai kyakkyawar hulda tsakaninsu da Rasha amma babu gaskiya game da jita-jitar jibge kayan yakin Wagner a cikin kasar.

A cewar sa basu san daga inda jita-jitar ta faro ba, amma babu mayakan Wagner bare kayakin aikinsu a cikin Burkina Faso.

A baya-bayan nan dai dambarwa tsakanin kasashen biyu musamman bayan bukatar Ouagadougou ta neman Faransar ta janye sojojinta daga kasar ya sanya Paris kiran jakadanta, wanda ya santa jita-jita kan yiwuwar samun bara kwatankwacin wadda aka samu tsakanin Faransar da Mali

Tun shekarar 2015 Burkina Faso ke fama da matsalar tsaro inda mayaka masu ikirarin jihadi ke kai hare-hare musamman a yankin arewacin kasar wanda ya fantsama har zuwa makwabta inda zuwa yanzu makamantan hare-haren ya kashe dubunnan mutane baya ga wasu miliyan 2 da tashin hankalin ya tilastawa barin matsugunansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.