'Yan ta'adda sun kashe sama da fararen hula 10 a Burkina Faso
Mutane sama da 10 ne suka mutu a sakamakon wasu jerin hare-haren da mayakan ta’addanci suka kai musu a yankin Dassa a cewar mahukuntan kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Bayanai sun ce maharan su kaddamar da harin ne kan fararen hula a garin da ke da nisan kilomita 140 daga babban birnin kasar Ougadougou, inda kuma suka hallaka mutane 12 nan take.
Burkina faso dai na cikin kasashen Sahara dake fama da ayyukan ta’addanci, da ya raba dubban fararen hula da jami’an tsaro da rayukan su, sai miliyoyin da suka zama ‘yan gudun hijira bayan guduwa don tsira da rayukan su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu