Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu sakamakon azumin mutuwa a Kenya ya kai 179

A jiya Juma’a ‘yan sandan tono karin gawarwaki 29 a gandun dajin Shakahola, adadi mafi yawa tun da aka fara tono gawarwaki a watan da ya gabata, a binciken da ake wa shugaban wata mujami’a da ya  umurci mabiyansa su yi azumin mutuwa don gaggawar saduwa da Yesu Almasihu.

Ministan cikin gidan Kenya, Kithure Kindiki, ya duba manyan kaburburan da aka binnne wadanda suka yi azumin mutuwa a gandun dajin Shakahola.
Ministan cikin gidan Kenya, Kithure Kindiki, ya duba manyan kaburburan da aka binnne wadanda suka yi azumin mutuwa a gandun dajin Shakahola. AP
Talla

An fara kashi na 2 na tono wadannan gawarwaki ne a wannan mako, bayan da wata tawaga karkashin jagorancin babban likitan gwamnati, Johansen Oduor  ta kammala gwaje-gwajen gawarwaki 112 da aka tono. An dakatar da tono gawarwakin ne sakamakon ruwan sama mai kama da baakin kwarya da ake yi a yankin.

A jiya Juma’a, ‘yan sanda suka sanar cewa babu wanda aka ceto da ransa, kuma zuwa yanzu mutane 25  ne kawai aka kama bisa zargin hannu a wannan aika-aika.

Kwamishinar ‘yan sandan yankin wadda ta bada sanarwar, Rhoda Onyancha, ta ce shugaban mujami’ar da wasu  mutane 25, wadnda suka taimaka wajen ganin babu wanda ya karya azuminsa na hannun hukuma.

Gwaje-gwajen da aka yi yi a gawarwakin mamatan ya nuna cewa a yayin da yunwa ce ta yi sanadin mutuwar mutanen da suka hadada yara da mata, an lura cewa an shake wasu, tare da yi wa wasu dukan tsiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.