Isa ga babban shafi

A yau Al'ummar Mauritania ke kada kuri'a a zaben kananan hukumomi

A yau Asabar al’ummar kasar Mauritania ke kada kuri’a a zaben da ake kallo a matsayin gwaji ga kamun ludayin  shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz, a yayin da kasashen duniya ke ki ci gaba da kira a gudanar da zabe mai inganci.

Wata Mata rufe da fuskan tana kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Mauritania
Wata Mata rufe da fuskan tana kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Mauritania REUTERS/Joe Penney
Talla

A karon farko kenan da masu zabe ke kada kuri’a a zaben kananan hukumomi tun bayan da shugaba Mohaamed Ould Abdel Aziz yah au karagar mulki a shekarar 2019.

Sai dai a yayin da ake shirin gudanar da wannan zabe, kungiyoyin kare hakkin dan adam irin su Amnesty International sun caccaki yadda gwamnatin kasar ke matsa wa ‘yan adawa, inda ta yi ta kama jagororin ‘yan adawa da kuma ‘yan jarida masu yaki da bauta.

Mauritania ce kasa ta karshe a duniya ta da haramta bauta a shekarar 1981, amma masu sharhi sun yi ittifain cewa haramcin na jeka-na – yi- ka ne, duba da yadda attajiran Larabawa ke ci gaba da bautar da kabilu bakaken fata.

Ana sa ran samun sakamkon zagaye na farko na zaben a cikin sa’o’i 48 bayan rufe rumfunar zabe. An kuma tsara za a gudanar da zabe zagaye na 2 a ranar 27 ga watan Mayu, don neman rabin kujeru 176 na majalisar dokokin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.