Isa ga babban shafi

Jagoran mulkin Sojin Burkina Faso na ziyara a Mali don tattaunawa matsalar tsaro

Jagoran mulkin Sojin Burkina Faso Laftanal Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba na ziyara a Mali yau asabar, ziyarar da ke matsayin karon farko da shugaban ke kai wa wata kasa tun bayan juyin mulkin a watan Janairu.

Jagoran mulkin Sojin Burkina Faso laftanal kanal Paul-Henri Damiba.
Jagoran mulkin Sojin Burkina Faso laftanal kanal Paul-Henri Damiba. via REUTERS - BURKINA FASO'S PRESIDENTIAL PRES
Talla

Wasu bayanai sun ce Damiba zai yi wata ganawa da jagoran mulkin Sojin Mali Kanal Assimi Goita, inda za su tattauna kan batutuwan da suka shafi matsalolin tsaron da suka dabaibaye kasashensu da kuma sabbin dabarun da za su yi amfani da su wajen murkushe ayyukan ta’addanci.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce bayan kammala ziyarar a Bamako kai tsaye jagoran zai wuce Ivory Coast a litinin mai zuwa inda zai gana da shugaba Alassane Ouattara duk dai dangane da matsalar tsaron da ke addabar kasashen na Sahel gabanin komawa Ougadougou a ranar.

Kasashen Sahel da suka kunshi, Mali Nijar da Burkina Faso na fama da matsalar hare-haren ta’addanci daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi tun daga shekarar 2012 inda a baya-bayan nan aka fara ganin fantsamuwar irin wadannan hare-hare a kasashen Ivory Coast da kuma Togo.

Ana ganin dai ziyarar ta Damiba ba ta rasa nasaba da yunkurin dawo da Mali cikin rundunar hadakar kasashen G5 Sahel da Faransa ke jagoranci a kokarin yakar matsalar tsaron yankin da suka kunshi kasashen ita Burkina Faso da Mali da Mauritania da Nijar da kuma Chadi.

A farkon shekarar nan ne Mali ta sanar da ficewa daga cikin rundunar ta G5 Sahel sai dai ko a watan jiya kasashen Nijar da Burkina sun roki kasar kan ta koma cikin rundunar don ci gaba da kakkabe matsalar tsaron yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.