Isa ga babban shafi

Malaman addini a Burkina Faso sun bukaci daina alakanta kabilar Fulani da ta'addanci

Daruruwan malaman addinin Islama a Burkina Faso sun yi tir da yadda wasu a kasar ke fakewa da rikice rikicen da ke faruwa da nufin mayar da shi rikicin kabilanci da kuma dorawa kabilar Fulani duk da laifin ta’addancin da aka aikata a kasar.

Wasu Fulani a Sahel.
Wasu Fulani a Sahel. AFP
Talla

Rikice-rikicen ‘yan ta’adda da kuniyoyi masu ikirarin jihadi na kara yaduwa a kasashen yankin sahel, lamarin da ake dora kusan kaso 90 cikin 100 na laifin a kan Fulani, abinda ke jefa fargaba a zukatan jama’a da tsoron kada rikicin ya juye zuwa fadan kabilanci.

Malaman addinin 700 da suka gudanar da wani taro na musamman a birnin Ouagadougou sun bukaci samar da sauyi ga salon yadda ake bayar da labaran da suka shafi ta’addanci ba tare da dora laifin kan wata Kabila ba.

A cewar Moussa Kounda shugaban Kungiyar Malaman addinin Islama a Burkina Faso, ya ce ta’addanci bashi da yare ko kabila wanda ke nuna cewa tsantsar rashin adalci ne karkata laifukan kan wata kabila.

Moussa Kuonda ya bayyana cewa wajibi ne garesu daukar matakan da suka dace don kawo karshen wannan matsala da wasu tsirarun kabilu musamman marasa rinjaye ke fuskanta.

Kungiyar Malaman ta kuma bukaci gwamnati ta bullo da sabbin dokoki don rage tasiri ko kuma kawar da wasu faya-fayan bidiyo da rubuce-rubuce da ke yawo a kafafen intanet wadanda ke alakanta kabilar Fulani da aikata laifukan na ta'addanci.

Kabilar Fulani wadda ke sahun kabily marasa rinjaye a Burkina Faso na da yawan jama'ar da ya kai mutum miliyan 1 da rabi a kasar mai yawan mutane miliyan 20 da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.