Isa ga babban shafi

Sojin Burkina Faso na shirin kai wani gagarumin hari

Burkina Faso ta sanar da shirinta na kaddamar da gagarumin farmaki don kakkabe ‘yan ta’adda a yankin Sahel da kuma gabashin kasar, bayan wa’adin makonni biyu da ta bai wa mazauna yankunan da su fice.

Sojojin kasar Burkina Faso.
Sojojin kasar Burkina Faso. © REUTERS/Luc Gnago
Talla

Babu takamamman rana da gwamnatin mulkin sojin kasar ta ware domin fara kai farmakin, sai dai ta ce cikin kwanaki masu zuwa.

Da ma dai hukumomi sun bai wa mazauna yankunan da ke cikin gandayen daji a gabashi da yankin Sahel da suka fice cikin makonni biyu, domin saboda mayaka masu ikirarin jihadi na samun mafaka a kauyukan.

Kwamandan rundunar soji ta musamman da zai jagoranci yaki da mayakan masu ikirarin jihadi, ya ce daga yanzu duk wanda aka samu a yankin tamkar dan ta’adda.

Yayin da ma’aikatar jinkai na kasar ta ce, ta karbi mutane da dama da suka fito daga kauyukan kuma ta sauke su a wasu sansani na musamman, tana basu kulawa.

Burkina Faso na daya daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da hare-haren daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.