Isa ga babban shafi

Sabon harin ta'addanci ya kashe Sojin Burkina Faso 15

Rundunar sojin Burkina Faso ta sanar da kisan Sojojinta 15 a wasu tagwayen hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi jiya talata, kwana guda bayan makamancinsa a kan iyakar kasar da Mali da ya kashe fararen hula.

Wani yanki na Burkina Faso mai fama da hare-haren ta'addanci.
Wani yanki na Burkina Faso mai fama da hare-haren ta'addanci. AFP - SIA KAMBOU
Talla

Tagwayen fashe-fashen sun afku ne a kan hanyar Bourzanga zuwa Djibo a yankin Tsakiyar Arewacin kasar ta Burkina Faso mai fama da hare-haren 'yan ta'adda.

Sanarwar ta kara da cewa "daya daga cikin motocin da ke cikin ayarin sojoji ce ta taka wani bam a kusa da gundumar Namsiguia a lardin Bam."

Yayin da kuma sojoji su ke kokarin tabbatar da tsaro da bayar da taimako ga wadanda abin ya shafa, sai aka tayar da bam na biyu daga nesa, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane da dama a wurin.

A shekara ta 2015 ne mayaka masu ikirarin jihadi da ke makwabciyar kasar Mali suka fara kai hare-hare kan iyakokin kasar Burkina Faso da Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.