Zanga-zangar adawa da kasancewar dakarun Faransa Burkina faso
A Ouagadougou babbam birnin kasar Burkina Faso, jama’a sun gudanar da zanga-zangar adawa da kasancewar dakarun Faransa wannan kasa a jiya asabar.
Wallafawa ranar:
Masu zanga-zangar lumana dauke da aluna sun taru a wurin nan mai dauke da sunan tsohon Shugaban sojin kasar Thomas Sankara da aka hallaka a shekara ta 1987 bayan wani juyin mulki da Blaise Compaore ya kitsa.
Masu zanga-zangar sun gayyaci daukacin yan kasar masu rajin kare Burkina Faso da son dawo da zaman lafiya a kasar na ganin sun sake fitowa ranar 12 ga watan Agusta a wani gaggarumin gangami da zai gudana birnin na Ouagadougou da nufin cewa Faransa da dakarun ta su fice daga wannan kasa kamar dai yadda Mali ta yi a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu