Isa ga babban shafi

ECOWAS za ta duba makomar takunkuman dake kan Mali, Burkina Faso da Guinea

Shugabannin kasashen yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS za su gudanar da taro domin tattaunawa kan makomar takunkuman da suka laftawa kasashe uku inda sojoji suka karbe mulki, da suka hada da Mali, da Guinea da kuma Burkina Faso.

Shugabannin kasashen ECOWAS a birnin Accra. 25 ga Maris, 2022.
Shugabannin kasashen ECOWAS a birnin Accra. 25 ga Maris, 2022. AP - Misper Apawu
Talla

A taron yini guda da za a yi a Accra, babban birnin Ghana, ECOWAS za ta yanke shawarar ko ya kamata takunkuman ladabtarwar su cigaba da aiki kan kasashen uku, ko kuma a janye su.

Wani makasudin taron kuma shi ne jaddada matsin lamba ga gwamnatocin sojin na Mali da Burkina Faso da kuma Guinea kan bukatar gaggauta gudanar da zabuka domin maidawa farar hula mulki.

Sojoji a kasashen uku sun yi juyin mulki hudu a cikin watanni 18, biyu a Mali a watan Agustan shekarar 2020 da Mayu a 2021, sai daya a kasar Guinea cikin watan Satumban 2021 da kuma juyin mulki daya a Burkina Faso a watan Janairun shekarar bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.