Isa ga babban shafi

Sojojin Burkina Faso biyar da 'Yan ta'adda talatin suka mutu yayin gumurzu

Akalla Sojojin biyar da ‘yan ta’adda 30 aka kashe a arewacin Burkina Faso, bayan wani kazamin hari da ake zargi mayaka masu ikirarin jihadi ne suka kai wani sansanin sojin kasar ranar Asabar.

Wasu jami'an tsaro Burkina Faso yayin wani aikin sintiri
Wasu jami'an tsaro Burkina Faso yayin wani aikin sintiri © AFP
Talla

Rundunar sojin Burkina Faso tace da safiyar wannan Asabar ne wani adadi mai yawa na ‘yan ta’adda dauke da manyan makamai suka kai kazamin hari sansanin su dake Bourzanga", wani yanki a lardin Bam da ke tsakiyar yankin arewa, "inda nan take suka maida martani.

Sanarwar tace, baya ga "Sojoji 5 da suka mutu wasu 10 sun samu raunuka yayin artabun".

Adadin farko yace, sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda aƙalla talatin yayin da saurann sunka rance na kare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.