'Yan bindiga sun tseratar da fursinoni 60 a farmakin gidan yarin Burkina Faso
‘Yan bindiga sun sako fursunoni kusan 60 a wani hari da suka kai wani gidan yari a arewa maso yammacin kasar Burkina Faso cikin dare, tare da kona motoci kafin su tsere.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da hukumomin tsaron kasar suka fitar ta ce mutanen dauke da makamai sun shiga garin Nouna ne da tsakar dare a kan motoci da kuma babura, inda suka yi ta harbin kan mai ‘uwa dawabi.
Burkina Faso dai na fama da hare-haren masu jihadi da suka yadu daga makwabciyarta Mali cikin shekaru goma da suka gabata, inda ake kai munanan hare-hare a duk mako.
Abin da bayanai ke cewa shine, an kashe dubban mutane a fadin kasar, kuma an tilasta wa miliyoyin jama’a kauracewa gidajensu, sakamakon hare-haren masu tayar da kayar baya.
Babu wanda ya rasa ransa a harin da aka kai gidan yarin, amma an harbe wani mayakin sa kai a cewar majiyoyin tsaro. An kuma kona motoci da babura da dama, baya ga yin barna a ofisoshin gidan yarin.
Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Wannan farmakin ya zo ne sa’o’i kadan bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe akalla mutane 11 a tsakanin garuruwan Dori da Gorgadji da ke arewacin kasar, kuma daga cikin wadanda suka mutu har da 'yan bindiga 9 da fararen hula biyu.
Rundunar sojin Burkina Faso a ranar Juma'a ta ce an kashe wasu sojoji 11 da 'yan bindiga da kuma jami'an 'yan sanda a wasu hare-haren da aka kai a cikin makon da ya gabata, amma sama da 'yan ta'adda 20 ne aka kashe a wani ramuwar gayya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu