Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Ta'addanci

Dakarun Burkina Faso 7 sun mutu sakamakon harin 'yan ta'adda

Rundunar sojin Burkina Faso ta ce dakarunta bakwai da kuma wasu ‘yan sa-kai hudu sun rasa rayukansu, yayin harin kwanton bauna har kashi biyu da ‘yan ta’adda suka kai musu a yankin arewacin kasar mai fama da matsalar tsaro.

Wani sojin Burkina Faso a yayin sintiri.
Wani sojin Burkina Faso a yayin sintiri. AFP PHOTO / SIA KAMBOU
Talla

Sanarwar da rundunar sojin Burkina Fason ta fitar a wannan Juma’a ta ce, an kai harin farko ne a kusa da garin Solle ranar Alhamis din da ta gabata inda sojoji biyu suka mutu da wasu farar hula hudu, ‘yan sa-kai da ke taimaka wa sojojin.

A wani harin na dabam kuma, dakaru  biyar ne suka halaka a dai ranar ta Alhamis a garin Ouanobe.

Sanarwar ta kara da cewa, mutane 9 ne suka jikkata, yayin da kuma aka gano gawarwakin maharan kimanin 20 lokacin da jami’an tsaro ke sintiri a wuraren da aka kai farmaki, bayan da suka tarwatsa ‘yan ta’adddan, tare da lalata makamansu da dama da kuma kwace wasu.

Tun daga shekarar 2015, kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS ke kai hare-hare a arewaci da gabashin Burkina Faso, inda suka kashe mutane sama da 2,000 tare da raba kusan miliyan biyu da muhallansu, tashin hankalin da ya shafi sassan Mali da Nijar da ke makwabtaka da kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.