Harin ta'addanci a sansanin soji ya lakume dakarun Burkina faso 5
Kimanin mutane 10, ciki har da sojoji 5 ne suka mutu a wani hari da aka kai wa wata cibiyar soji a Burkina Faso a yau Lahadi.
Wallafawa ranar:
Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfani dillancin labaran Faransa cewa da misalin karfe 5 na asubahin yau wata kungiyar ‘yan ta’adda ta kai farmaki kan sansanin sojin Gaskinde a lardin Soum, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 10.
Majiyar ta ce saura wadanda suka mutu fararen hula ne, kana daga bisani wani jami’in gwamnati a yankin ya tabbatar da mutuwar fararen hula 4.
Kungiyoyi masu ikirarin jihadi da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS sun yi ta kaddamar da hare hare a arewaci da gabashin Burkina Faso tun daga shekarar 2015, abin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane dubu 2 tare da daidaita kusan miliyan 2.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu