Isa ga babban shafi

Yunwa na kara tsananta a Burkina Faso - MSF

Mazauna wani gari da ke arewacin Burkina Faso wanda mayakan jihadi suka mamaye hanyar shiga yankin, sun ce kayan abinci ya kare musu.

Hukumomi na duniya sun yi ittifakin cewa matsalolin mayakan jihadi na kara ta'azzara a wasu kasashen Afirka.
Hukumomi na duniya sun yi ittifakin cewa matsalolin mayakan jihadi na kara ta'azzara a wasu kasashen Afirka. Getty Images/iStockphoto - Stas_V
Talla

A ranar 25 ga watan Yuni ne mayakan jihadi suka lalata wata gadar da ta kasance hanya daya tilo wajen shiga garin Sebba, cibiyar gudanarwar kasuwanci na lardin Yagha.

Mazauna garin sun yi kokarin gyara barnar da aka yi cikin gaggawa amma gadar ta ruguje a wani harin da aka kai musu, abin da ya janyo rashin hanyar fita daga garin.

kungiyar likitoci ta kasa da kasa MSF ta tabbatar da cewa tsananin yunwa na kara tsananta a yankin.

Wani mazaunin kauyen na Sebba, Mohamed Dicko, ya ce gadar ba wai kawai tana da mahimmanci ga garin ba amma ga har da yankunan lardin Yagha, ciki har da Solhan da Mansila.

Sebba, mai yawan jama'a 30,000, ya zama mafaka ga mutane a yankin Yaghan wadanda suka tsere daga gidajensu saboda hare-haren masu jihadi.

Burkina Faso, wadda ta kasance daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya, ta fara fuskantar hari a shekarar 2015 daga mayakan jihadi da ke aiki a makwabciyarta Mali.

Tun daga wannan lokacin dubban mutane suka mutu, kusan miliyan biyu suka rasa matsugunansu, kuma sama da kashi uku na yankunan kasar na hannun gwamnati, a cewar alkaluman hukumomi.

Hare-haren sun karu ne tun farkon wannan shekara, duk kuwa da juyin mulkin da sojoji suka yi, wadanda suka bayyana manufarsu shine inganta sha’anin tsaron kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.