Mata na taimakawa kungiyoyin yan ta'adda a Burkina Faso
Hukumomin Burkina Faso a jiya juma’a sun bayyana damuwa da takaici ganin ta yada ake samun mata dake dafawa mayakan jihadi a hare-haren da suke kai cikin kasar.
Wallafawa ranar:
Minista kula da jinsi da iyalin na kasar ta Nurkina Faso Salimata Nebie ce ta sanar da haka yayin wani taron manema labarai.
Jami’ar gwamnatin ta bayyana cewa kasancewar mata da kungiyoyin yan ta’adda a wannan lokaci,na daf da zama ruwan dare a wani lokaci da hukumomi ke iya kokarin su don ganin an magance matsallar ta’addanci da rashi tsaro a fadin kasar ta Burkina Faso.
A karshe Ministar ta bayyana cewa biyo bayan harin ta’addanci da wasu tsageru suka kai wa ayarin sojin kasar ranar 25 ga wannan watan da muke cikin sa a yankin Kelbo dake arewacin kasar , an hango mata na kwashe gawarwakin mayankan jihadi tareda kai dauki ga wandada suka jikata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu