Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya kashe fararen hula 27 a Burkina Faso

Rahotanni daga Burkina Faso sun bayyana yadda wasu tagwayen hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi a kauyukan arewacin kasar ya hallaka fararen hula 27.

Hare-haren ta'addanci na ci gaba da tsananta a Burkina Faso.
Hare-haren ta'addanci na ci gaba da tsananta a Burkina Faso. AFP/Olivia de Maismont
Talla

Wasu alkaluman gwamnatin Burkina Faso game da hare-haren na baya-bayan nan a yankin arewaci sun nuna cewa cikin cikin wadanda 'yan ta'addan suka kashe kar da kananan yara 15 ko da ya ke wasu rahotanni na cewa adadin yaran ya haura 20.

Bayanai sun ce da misalin karfe 5 na yammacin jiya lahadi ne gungun mayakan suka farmaki kauyen Boussa da ke lardin Kossi a arewacin Burkina Faso, inda suka rika harbin iska gabanin komawa kauyen da dare tare da kisan tarin mutane.

Wani jami’in tsaro da ya bukaci a sakaya sunansa a yankin, ya ce ko a Asabar din da ta gabata sai dai harin 'yan ta'addan ya kashe mutane 12 a kauyen Namissiguima da ke lardin Yatenga na kasar ciki har da mayakan sa kai 3.

Burkina Faso guda cikin matalautan kasashen nahiyar Afrika, na fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi a yankin Arewaci tsawon shekaru galibi daga mayakan da ke kwararowa kasar daga makwabciyarta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.