Burkina Faso: Zaman makoki na kwanaki 3 bayan harin ta'addanci
Akalla mutane 79 ne ‘yan ta’adda suka kashe a Seytenga dake arewacin Burkina Faso, al’amari mafi muni tun bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Lionel Bilgo ya bayyana a jiya Litinin.
Wallafawa ranar:
Bilgo ya ce ya zuwa yanzu sojoji sun gano gawarwaki 79 bayan da aka kai hari a kauyen Seytenga a cikin daren Asabar, inda ya kara da cewa adadin na iya karuwa.
Ya shaida a wani taron manema labarai cewa ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa da su sun koma kauyen, k,um aba mamaki sun tafi da wasu gawarwaki.
A garin Seytenga ne aka yi mummunan bata kashi a makon da ya gabata, inda aka samu sarar rayuka.
An kashe jandarmomi 11 a ranar Alhamis a wannan gari, lamarin da ya wajabta wani sintirin soji da ya yi sandin mutuwar mayaka masu ikirarin jihadi guda 40.
Kungiyoyin agaji a yaankin sun ce kimanin mutane dubu 3 ne aka bai wa mafaka a garuruwan da ke makwaftaka da kauyen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu