Isa ga babban shafi

Mahara sun kashe jami'an tsaron Burkina Faso11 a kan iyaka da Nijar

Akalla jandarmomi 11 ne mahara dauke da makamai suka kashe a kauyen Setenga dake lardi Seno na kasar Burkina Faso a wani hari da suka kai marecen jiya alhamis.

Jandarmomi 10 ne suka mutu  a wani harin yan bindiga a Burkina Faso
Jandarmomi 10 ne suka mutu a wani harin yan bindiga a Burkina Faso © RFI
Talla

Hukumomin tsaron kasar ta Burkina Faso sun tabbatar da wannan sabon harin da mayakan jihadi suka kai wannan yanki a wani lokaci da majalisar soji dake rike da madafan ikon kasar ke fuskantar mantsin lamba daga waje da cikin kasar a sha'anin da ya shafi tsaro da siyasa,musaman a wani lokaci da kungiyar kasashen Ecowas ke fatan samun tabbaci daga majalisar sojin Burkina na sake mika mulki ga farraren hula.

Jami'an tsaron Burkina Faso
Jami'an tsaron Burkina Faso © AFP

Wannan hari na baya-bayan nan ya yi sanadiyyar mutuwar Jandarmomi 11 a Seytenga,wanda ke nuna karara durkushewar sha'anin tsaro a arewacin kasar duk da kokarin al'uma da suka dau niyar kaffa kungiyar yan sa kai tare da gundumuwar hukumomin Burkina Faso.

Burkina Faso na daga cikin kasashen yankin Sahel da suka hada da Nijar,Mali hata arewacin Jamhuriyar Benin na fuskantar hare-haren mayakan jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.