Isa ga babban shafi

An kashe fararen hula a Burkina Faso

Akalla mutane 40 ne galibi fararen hula da ke aikin sa-kai da kuma sojoji suka rasa rayukansu a wani hari da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai arewacin Burkina Faso, harin da ke zuwa daidai lokacin da ‘yan ta’addan ke zafafa hare-herensu kan jami’an tsaro a kasar.

Wasu jami'an tsaron Burkina Faso
Wasu jami'an tsaron Burkina Faso © AFP
Talla

Jagoran mayakan sa-kai na kungiyar VDP ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, a Asabar din da ta gabata kadai, harin mayakan ya hallaka mutane 25 ciki har da mambobinsu 13.

Majiyoyin tsaro da ke tabbatar da hare-haren ta’addancin sun kuma bayyana yadda makamancin harin ya kashe mutane 15 a Kompienga da ke yankin kudu maso gabashin iyakar Burkina Faso da kasashen Togo da Benin lokacin da jami’an tsaron sa-kan ke rakiyar wata tawagar motoci.

Shaidun gani da ido sun ce, mayakan sa-kai 3 suka mutu a farmakin wanda ke matsayin kari kan kwantan baunar da ‘yan ta’addan suka yiwa ‘yan sanda da jami’an Jandarma a Faramana gab da iyakar kasar da Mali wanda ya jikkata jami’an tsaro 2.

Burkina Faso guda cikin matalautan kasashe a nahiyar Afrika na fama da hare-haren ta’addanci ne tun daga shekarar 2015 lokacin da mayaka masu ikirarin jihadi suka fara fadada hare-harensu daga Mali zuwa makwabta lamarin da zuwa yanzu ya hallaka mutane dubu 2 tare da tilastawa wasu miliyan 2 tserewa daga muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.