Isa ga babban shafi

Jama'a sun fusata a arewacin Burkina Faso sabili da rashin tsaro

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga lumana jiya asabar a garin Pama dake lardin Kompienga dake gabashin kasar Burkia Faso da nufin nuna takaici da damuwar su ganin ta yada  mahara ke ci gaba da afkawa mazauna wadanan yankuna.

Sojoji daga Burkina Faso yayin sintiri a kan hanyar Gorgadji a Burkina Faso, Maris 3, 2019.
Sojoji daga Burkina Faso yayin sintiri a kan hanyar Gorgadji a Burkina Faso, Maris 3, 2019. © REUTERS/Luc Gnago
Talla

Masu zanga-zangar sun samu goyan bayan shugabanin addinai,Sarakunan gargajiya, kungiyoyin farraren hula ,suka kuma yi amfani da wannan dama tareda rubuta wasika ga babban jami’in gwamnati na yankin don nuna masa rashin ko in kula da majalisar soji ke yi dangane da batun tsaro a wannan yaki  da yan ta’adda.

Burkina Faso da wasu kasashen yankin Sahel na fama da wannan matsala ta yan ta'adda,al'amarin da ya durkusar da lamuran da suka shafi  tattalin arziki,kasuwanci.ilimi da kiwon lafiya ga baki daya.

A wasu yankunan kasar ta Burkina Faso musaman arewacin  kasar,sheidu sun tabbatr da cewa jami’an tsaro sun bar wurare ga baki daya ga hannun yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.