Isa ga babban shafi

An gano gawar wani babban jami'in Burkina Faso da aka sace

Majojin tsaro a Burkina Faso sun bayyana cewa, an gano gawar wani babban jami'in gwamnati da aka yi garkuwa da shi a yammacin kasar mai fama da mayaka masu ikirarin jihadi.

Wasu dakarun Burkina Faso a Ouagadougou, 1/10/23
Wasu dakarun Burkina Faso a Ouagadougou, 1/10/23 REUTERS - VINCENT BADO
Talla

Ma’aikatar cikin gidan Burkina Faso tace Amadou Kabore, wanda shine babban wakilin gwamnati  a yankin Boucle du Mouhoun, ya mutu ne a ranar Litinin, batare da karin haske kan mutuwarsa ba, sai dai ta sanar da jana'izar sa da aka yi Laraba a tsakiyar garin Tanghin-Dassouri.

Mazauna yankin da suka nemi a sakaya sunansu sun ce an yi garkuwa da Kabore ne ranar Litinin bayan wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun tare motarsa a kusa da kauyen Karo a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Tcheriba, inda acan kuma magajin gari ne shi.

Wani abokin aikin Kabore da direban sa sun samu nasarar tserewa, amma daga baya an tsinci gawar kwantoman a wani dajin da ke kusa, kamar yadda majiyar tsaro ta bayyana.

A watan da ya gabata, rundunar sojin kasar ta ce ta kai wani samame na tsaro a yankin, inda ta hada sojoji sama da 800 da mambobin kungiyar sa kai ta VDP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.